Kotu ta amince a karbe dukiyoyin tsohon Gwamna Mu’azu Babangida Aliyu

Kotu ta amince a karbe dukiyoyin tsohon Gwamna Mu’azu Babangida Aliyu

A cikin makon nan ne mu ka samu labari cewa babban Kotun Najeriya da ke Garin Minna a cikin Jihar Neja ta amincewa Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa watau EFCC ta karbe wasu kadarorin Mu’azu Babangida Aliyu.

Daga cikin kayan da za a karbe daga hannun tsohon Gwamnan na Jihar Neja Dr. Mu’azu Babangida Aliyu akwai makudan kudi da gidaje da gonaki da dai sauran su.

Kotu ta amince a karbe dukiyoyin tsohon Gwamna Mu’azu Babangida Aliyu

Ana zargin tsohon Gwamna Mu’azu Babangida Aliyu da yin sama da fadi

Ga dai jerin kayan da za a raba tsohon Gwamnan da su:

KU KARANTA: Jerry Gana ya fito takarar Shugaban kasa a 2019

1. Manyan gidajen sa 2 a cikin Garin Minna a cikin Jihar Neja

2. Makekiyar gonar sa mai dauke da dakuna iri-iri

3. Gidajen tarbar baki da hutu 4 a Jihar Neja

4. Makudan kudi har Naira Miliyan 57

5. Manyan motoci kirar ‘jeep’ mai suna Prado har guda 4

Yanzu dai Gwamnatin Tarayya za ta karbe kadarorin har zuwa lokacin da za a kammala shari’a. Alkali mai shari’a Yellim Bogoro ya yanke wannan hukunci, Ana zargin Gwamnan da wani Umar Nasko ne da satar kudi fiye da Naira Biliyan 1.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel