Dandalin Kannywood: Jaruma Rahama Sadau ta tayar da kura a shafukan sada zumunta da sabbin hotuna
Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood, Rahama Sadau ta wallafa wasu kayatattun hotunan ta a shafukan sada zumuntar ta da suka burge jama'a da dama musamman ma masoyan ta.
Hotunan wandanda ke dauke da surar jarumar sanye da doguwar riga ja a cikin wani gida kayatacce yayi matukar daukar hankalin mabiyan jarumar inda suka yi ta tofa albarkacin bakin su game da hotunan.
KU KARANTA: Yadda zamu fitar da dan takarar mu na shugaban kasa - PDP
Legit.ng ta samu cewa a kwanan baya dai jarumar ta dan shiga cakwakiya biyo bayan fitar wani faifan bidiyon waka tare da mawaki Classiq inda aka nuna su suna rungumar juna.
Wannan ne ma ya jawo har kungiyar masu wasan Hausa din ta MOPPAN suka dakatar da ita kafin daga bisani ayi mata afuwa bayan ta nemi gafara.
Yanzu haka dai jarumar na daya daga cikin jaruman masana'antar da tauraruwar su ke matukar haskawa.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng