Dandalin Kannywood: An shawarci matan Arewa da suyi koyi da dabi'un Rahma Sadau
Wata gamayyar kungiyoyin matan dake daukacin jahohi 19 na Arewacin Najeriya sun shawarci dukkanin matan dake a yankin na Arewacin Najeriya da suyi koyi da kyawawan halayen jarumar nan ta fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood watau Rahma Sadau.
Gamayyar kungiyoyin dai sun yi wannan kiran ne jim kadan bayan sun kammala taron su da suka sabayi a lokaci lokaci inda kuma suka nuna sha'awar ta su fili karara ga halayen na jarumar da suka bayyana cewa masu kyau ne kuma abun sha'awa.
KU KARANTA: Mata a Kaduna sun yi wa Sanata Shehu Sani zanga-zanga
Legit.ng dai ta samu cewa matan sun shawarci daukacin matan Arewar da su rike sana'ar duk da suke yi sosai ba tare da damuwa da cece-kucen da jama'a za su rika yi masu ba tamkar dai yadda jarumar ta ke cikin yi.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa kungiyar masu shirya fina-finan na Hausa a baya sun dakatar da jaruma Rahma Sadau daga yin fim saboda abunda suka kira saba dokar su da ta yi yayin da ta rungumi mawaki a cikin wata waka da suka yi.
Asali: Legit.ng