Ban iya karatu da sauri ba – Buhari

Ban iya karatu da sauri ba – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin takwaransa na kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa.

A ganawar ta su shugaba Buhari ya amince cewa ya kasa sa hannu kan yarjejeniyar yin kasuwanci ba tare da shinge ba na nahiyar Afirka, saboda "ba ya iya karatu da sauri."

Shugaba Buhari ya ce yana da aniyar sa hannu kan yarjejeniyar da shugabannin Afirka suka rattaba hannu a kai a kasar Rwanda a watan Maris, nan ba da jimawa.

A cewar shugaban kasar "Ba na iya karatu da sauri, watakila saboda ni tsohon soja ne. Ban karanta yarjejeniyar cikin sauri ba, kafin jami'aina suka ce ya kamata na sa hannu."

KU KARANTA KUMA: An binne mutane 32 da yan fashi suka kashe a Sokoto (hoto)

Ya kara da cewa "Na ajiye takardar kan taburina. Kuma zan sa hannu a kai nan ba da jimawa ba."

A wani lamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kaddamar da layin dogo da tashan jirgin kasan birnin tarayya Abuja a yau Talata, 12 ga watan Yuli.

A wani jawabi da shugaban kasar ya wallafa a shafin sada zuminta na Facebook ya bayyana cewa wannan hanyar sufuri ne wanda zai saukaka rayuwa ga mazauna birnin tarayya tare da habbaka tattalin arziki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel