An samu barkewar hargowa da yamutsi a zauren majalisa saboda ambaton R-APC

An samu barkewar hargowa da yamutsi a zauren majalisa saboda ambaton R-APC

- An samu barkewar hargowa da yamutsi a zauren majalisa saboda ambaton R-APC

- Yamutsin ya fara ne bayan mamba a majalisar ya gabatar da kansa a matsayin me alfahari da jam'iyyarsa ta R-APC

- Saidai kafin boren ya yi nisa, kakakin majalisar, Yakubu Dogara, ya shawo kan lamarin

Mambobin majalisar wakilai ta kasa 'yan jam'iyyar APC sun yi boren yayin zaman majalisa na yau, Laraba, saboda ambaton tsagin R-APC a zauren majalisar.

Saidai kafin boren ya yi nisa, kakakin majalisar, Yakubu Dogara, ya shawo kan lamarin.

An samu barkewar hargowa da yamutsi a zauren majalisa saboda ambaton R-APC
Zauren majalisa wakilai

Yamutsin ya fara ne bayan mamba a majalisar, Mista Bode Ayorinde, ya gabatar da kansa a matsayin me alfahari da jam'iyyarsa ta R-APC.

Amma, wani mamba a majalisar, Mohammed Bago, ya katse masa hanzari ta hanyar shaida masa cewar majalisar ba ta da masaniyar wata jam'iyya mai suna R-APC.

DUBA WANNAN: Wasu jam'iyyu 20 sun hada gwuiwa da APC domin marawa Buhari baya

Da yawan 'ya'yan jam'iyyar APC a zauren majalisar sun goyi da bayan Bago tare da hana Ayorinde cigaba da magana.

Ana tsaka da wannan hargowa da yamutsi ne Dogara ya saka baki tare da kwantar da hayaniyar da ta barke.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng