Da duminsa: ‘Yan Boko Haram 113 da matansu sun gamu da fushin kuliya, an yanke masu hukunci

Da duminsa: ‘Yan Boko Haram 113 da matansu sun gamu da fushin kuliya, an yanke masu hukunci

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a Kainji, jihar Neja, ta yankewa wasu ‘yan Boko Haram 113 da matansu na aure hukuncin daurin a gidan yari saboda samun su da hannu cikin aiyukan ta’addanci.

Wata majiya a ma’aikatar shari’a dake aiki a Kainji ta shaidawa jaridar daily Trust cewar an samu wadanda aka gurfanar din da laifin zama ‘yan kungiyar ta’addanci tare da boye muhimman bayanai da kan iya amfanar hukuma wajen bincike a kan ragowar masu aiyukan ta’addanci.

Da duminsa: ‘Yan Boko Haram 113 da matansu sun gamu da fushin kuliya, an yanke masu hukunci
‘Yan Boko Haram

Daga cikin wadanda aka yankewa hukuncin akwai wani Kabiru Mohammed, dan asalin karamar hukumar Funtua ta jihar Katsina, da kotu ta aike zuwa gidan yari na tsawon shekaru 30 saboda samun shi da laifin karbar horo tare da hada bama-baman da kungiyar Boko Haram tayi amfani das u wajen wasu hare-hare da ta kai a garuruwan Bama, Konduga, Baga na jihar Borno da kuma garin Damaturu na jihar Yobe.

DUBA WANNAN: Kiyayewar Allah: dakarun soji sun kashe wutar wani rikicin kabilanci da ya so barkewa a jihar Gombe

Kazalika kotun ta yankewa Zainab, matar wani kwamandan kungiyar Boko Haram, Babawa, hukuncin daurin shekaru hudu.

An kama Zainab ne a shekarar 2014 yayin da take kan hanyarta ta zuwa wurin mijinta dake boye a sansanin ‘yan Boko Haram dake dajin Sambisa.

Mijinta, da aka fi sani da Idoko ko Nagada, na daga cikin kwamandojin kungiyar Boko Haram 156 da sojojin Najeriya k enema ruwa a jallo.

Akwai karin bayani....

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel