Jakadar Najeriya ta kasar Sao Tome and Principe ta rasu

Jakadar Najeriya ta kasar Sao Tome and Principe ta rasu

Mun samu labari cewa Jakadar Najeriya zuwa Jamhuriyyar Sao Tome and Principe ta rasu shekaran jiya. Queen Worlu ta cika ne a Ranar 9 ga watan nan ta na bakin aikin ta a kasar waje.

Kamar yadda labari ya zo mana Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika ta’aziyyar sa ga Iyalun Queen Worlu na rashin ta da aka yi. Shugaban kasar ya kuma yi wa Mutanen Jihar Edo da na Kasar nan baki daya ta’aziyyar rashin ‘Diyar su.

Garba Shehu wanda shi ne ke magana da yawun Shugaban kasar ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar a jiya Talata a babban Birnin Tarayya Abuja. Shugaban kasar ya nemi a kawo gawar wannan Baiwar Allah gida a jirgin saman kasar.

KU KARANTA: Wasu Gwamnonin Arewa da ba a taba bincike ba

An dai yi babban rashin wannan mata wanda ta fi shekara 30 tana aiki a kasasehn waje. Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Queen Worlu a matsayin Jakadan kasar zuwa Kasar Sao Tome ne a 2017 bayan tayi aiki iri-iri da kasashen waje.

Shugaban kasar dai yace yayi takaicin wannan babban rashi na Marigayiya Worlu wanda yace tayi wa kasar ta Najeriya bakin kokarin ta a wajen aiki. Shugaba Buhari yayi addu’a Ubangiji ya ba Iyalin ta hakurin babban rashin da aka yi.

Idan ba ku manta ba mun samu labari cewa babban ‘Dan kasuwar nan Femi Babalola ya fito neman takarar kujerar Shugaban kasa inda yace shugabancin kasar nan sai da irin su idan za ayi gyara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng