Badakalar NYSC: Ana shirya makarkashiya domin ba Minista Adeosun gaskiya

Badakalar NYSC: Ana shirya makarkashiya domin ba Minista Adeosun gaskiya

Mun fahimci cewa wasu manya a Hukumar NYSC na kasar nan na kokarin tsallakar da Ministan kudin kasar nan Kemi Adeosun daga badakalar da ta shiga na amfani da takardun shaida na bogi.

The Cable ta rahoto cewa wasu Jami’an Hukumar NYSC na neman hanyar da za su yi domin fitar da Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun daga cikin badakalar da ta shiga. Idan ba haka ba dai Ministar kasar tana cikin ruwan zafi.

Badakalar NYSC: Ana shirya makarkashiya domin ba Minista Adeosun gaskiya

Ana zargin Ministar kudi Adeosun da rashin gaskiya

Labarin da mu ke samu shi ne ta kai yanzu ana neman daura laifin kan wani tsohon Shugaban NYSC da ya rasu tun kwanaki. Hukumar NYSC dai za ta daurawa Birgediya Janar Yusuf Bomai ne wanda ya rasu tun bara laifin komai kan batun.

A takardar shaidar Ministar, Janar Yusuf Bomai ne ya sa hannu duk da cewa a lokacin Janar din ya bar kujerar Shugaban NYSC. A karshen 2009 dai Maharazu Tsiga ne Shugaban Hukumar kuma sa hannun sa ya kamata a gani ba Bomoi ba.

KU KARANTA: An hurowa Minista Buhari Adeosun kan zargin NYSC

Yanzu dai komai ya faru Marigayi Birgediya Janar Yusuf Bomai ba zai iya wanke kan sa ba don ya rasu tun tuni. Hukumar za ta nemi tace Marigayin ne yayi kuskure wajen ba Adeosun satifiket din ko kuma wata matsala dabam aka samu.

Kemi Adeosun ba tayi wa kasa hidima ba inda ake zargin ta fake da cewa shekarun ta sun zarce ko da dai lokacin da ta kammala Jami’a tana shekara 22 ne kacal. Wannan dai ya saba dokar kasar kuma bai hallatta a ba mutum kowane irin aiki ba.

Jiya dai kun ji cewa Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun ba ta ce komai ba har yanzu bayan an dauki kwanaki ana zargin ta. Hukumar NYSC ta fito tayi magana jiya inda tace za ta bincike amma har yanzu shiru. Binciken dai bai kamata ya jima ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel