PDP da wasu jam’iyyu 33 sun hada karfi wuri guda, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya
Jam’iyyar Adawa da PDP da wasu jam’iyyun Najeriya 33 su hadu a wani dakin taro dake Musa Yar Adua a Abuja domin saka hannu a kan yarjejeniyar yin aiki tare domin kwace mulki daga hannun jam’iyyar APC mai mulki.
Yayin taron nasu, jam’iyyun sun rattaba kan yarjejeniyar marawa dan takara guda baya da zai fafata da shugaba Buhari da zai yiwa jam’iyyar APC takara.
Cikin jami’yyun da suka halarci taron akwai, SDP, NCP, ADC, da kuma jami’yyar adawa ta Labour.
Daga cikin jiga-jigan ‘yan siyasa da suka halarci wurin taron nay au akwai shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da Buba Galadima; shugaban sabuwar jam’iyyar R-APC da ta balle daga APC, da kuma jagoran nPDP, Kawu Baraje.
DUBA WANNAN: 2019: Sanatoci 12, mambobin majalisar wakilai 70 sun dira Kaduna domin nuna goyon baya ga Buhari
Ya zuwa yanzu ba a san wane bangare ne zai fitar da dan takarar shugabancin kasa da zai wakilci hadakar jam’iyyun ba. Alamu dai na nuna cewar mai yiwuwa jam’iyyar PDP ce zata fitar da dantakara, su kuma tsagin R-APC su kawo mataimaki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng