Wuya tayi wuya: 'Yan Boko Haram sun tsere sun bar wata yarinya Sojoji sun ceto ta

Wuya tayi wuya: 'Yan Boko Haram sun tsere sun bar wata yarinya Sojoji sun ceto ta

- Sojojin Najeriya sun samu nasarar kawato bindigu da harsasai a hannun 'yan Boko Haram

- Bayan makaman kuma sunyi nasarar kwato wata yarinya da suka gudu suka barta

- Kamar yadda kakakin rundunar ya tabbatar

Rundunar sojin kasar nan a jihar Borno sun yi nasarar kubutar da wata yarinya daga hannun yan tada kayar baya na Boko Haram, kamar yadda mai magana da yawun bakin Rundunar sojin Birigediya-Janar Texas Chukwu ne ya bayyana hakan a yau litinin.

Wuya tayi wuya: 'Yan Boko Haram sun tsere sun bar wata yarinya Sojoji sun ceto ta
Wuya tayi wuya: 'Yan Boko Haram sun tsere sun bar wata yarinya Sojoji sun ceto ta

Chukwu ya yi wannan jawabin ne a wani sumaman sharar daji da suka yi "An samu bindigogi kirar AK47 har guda uku sai kuma tarin harsashi mai yawa tare da riga mai dauke da bam".

KU KARANTA: Matsalar rashin tsaron jihar Zamfara ya rutsa da wani Dagaci, ‘yan bindiga sun aika shi barzahu

"An samu kayan hada bam da dama wanda suka hada da batirin waya, da bam din hannu, sai batirin mota kirar volt guda biyu da sauran abubuwan kayan hada bam". Kamar yadda kamfanin dillacin labarai (NAN) ya rawaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng