An maidawa Sheikh Gumi martani na cewa sha’anin tsaro ya cabe a Najeriya

An maidawa Sheikh Gumi martani na cewa sha’anin tsaro ya cabe a Najeriya

Wani babban Malamin addini da ma Boko a Arewacin Najeriya Farfesa Salisu Shehu yayi wa fitaccen Malamin addinin Musuluncin nan watau Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi raddi na cewa abubuwa sun tabarbare a Najeriya.

An maidawa Sheikh Gumi martani na cewa sha’anin tsaro ya cabe a Najeriya
Sheikh Gumi yace gara lokacin Jonathan a kan yanzu

A wata hira da Babban Malami Ahmad Abubakar Mahmud Gumi yayi da Jaridar Punch ya bayyana cewa sha’anin tsaro ya jagule sannan kuma harkar kiwon lafiya da sauran su duk sun cabe a lokacin Gwamnatin nan ta Shugaba Buhari.

KU KARANTA: Abin da ya sa wasu ke goyon bayan Shugaba Buhari a Najeriya

Babban Malamin wanda yana cikin Majalisar koli ta addinin Musulunci a Najeriya tace akwai alamun karya a maganar da Malamin yayi na cewa sha’anin tsaro ya fi kyau a lokacin tsohon Shugaban kasa Jonathan yana mulkin kasar.

Farfesan yace a lokacin Jonathan sai da ta kai bangare da daman a Arewacin Kasar sun shiga hannun ‘Yan Boko Haram. Malamin yace Sheikh Gumi bai isa ya je irin su Maiduguri, Yola. Damaturu da sauran su yayi wannan magana ba.

Malamin na Jami’ar Bayero ta Kano ya nemi Malamin yayi wa Gwamnatin Buhari adalci kamar yadda addinin Musulunci ya koyar. Farfesa Shehu ya tunawa Gumi irin ta’adin da aka yi a Arewa ta wani dogon rubutu da yayi a a Facebook.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng