Hadakar kungiyoyin Islama na Najeriya: Makarkashiya ce ake yi don kada shugaba Buhari a zabukan badi ake fakewa da kashe-kashe

Hadakar kungiyoyin Islama na Najeriya: Makarkashiya ce ake yi don kada shugaba Buhari a zabukan badi ake fakewa da kashe-kashe

- NSCIA su ke kokarin dawo da Islama kan ganiyarsa a kasar nan

- Suna goyon bayan shugaba Buhari a siyasance

- Suna ganin makarkashiya ake yi don kawar da Islama daga karfi

Hadakar kungiyoyin Islama na Najeriya: Makarkashiya ce ake yi don kada shugaba Buhari a zabukan badi ake fakewa da kashe-kashe
Hadakar kungiyoyin Islama na Najeriya: Makarkashiya ce ake yi don kada shugaba Buhari a zabukan badi ake fakewa da kashe-kashe

Kungiyar koli ta shari'ar musulunci ta Najeriya tayi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo tsaro ga kauyuka tare da gyara yanayin tsaro na kasar.

Tayi kiran ne a wata takarda da ta sa hannu ta hannun mataimakin sakataren ta, Salisu Shehu, a lokacin da kungiyar ke nuna damuwarta game da kashe kashen da ya yawaita a kasar.

Kungiyar musuluncin ta nuna damuwarta akan kashe kashen da ya bazu a fadin kasar. Ta kwatanta kashe kashen da rashin tausayi, mugunta da kuma shaidanci.

Ta nuna bacin ran ta game da wadanda aka biya don su canza ma mutane tunani. Domin suna nuna musulmai ne yan ta'addan da ake lika wa kashe kashen makiyaya.

"Akwai isassun shaidu dake nuna cewa cewa musulthe mai ne aka kawo, ashe, mafi yawa ma wadanda aka tsayar a manyan hanyoyi"

Abin ban haushin shine mutanen da suka kashe musulmai ranar sallah a wasu shekaru da suka gabata, sune da wannan mummunan aikin. Inji kungiyar

Ta jinjiinawa kungiyar mabiya addinin kirista ta Najeriya, reshen jihar Bauchi akan tsokacin da tayi akan abinda ya faru.

DUBA WANNAN: Zaki yayi danyen hukumci kan wasu mafarauta

Kamar yadda chiyaman din CAN na jihar, Reverend Joshua Ray Miller yace, harin dai aikin yan bangar siyasa ne, masu son bata gwamnatin shugaban Muhammadu Buhari domin cimma wata manufar su a zaben 2019.

Chiyaman din yace abin haushi ne ace wasu na boyewa karkashin tutar Fulani makiyaya don tada tarzomar da wasu yan siyasa marasa kishin kasa suka basu kwangila.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng