An kamo dansandan da ya kashe kopa, an garqame shi kafin a kammala bincike
- Ranar Alhamis Linda zata kammala bautar kasar da take a garin Abuja kafin mutuwar ta
- Yan sandan sunce akan mene motar taki tsayawa bayan da yan sandan suka tsayar dasu
- Yar uwar mai rasuwar, Chinenye tace yan sandan har yanzu basu fada musu dalilin harbin Igwetu ba da dan sandan yayi
Hukumar yan sandan Gwamnatin tarayya ta garkame wani jami'in Dan sanda, Benjamin Peter, da zargin harbin wata yar bautar kasa, Linda Igwetu, a Abuja ranar laraba da safe.
Mun samu labarin cewa anyi binciken mutuwar mai shekaru 22 a duniya, wacce aka kashe sakamakon motar da take ciki tare da abokan aikin ta biyu ta kasa tsayawa a wani gurin binciken yan sandan, wanda ya kawo sanadin harbin da Dan sandan yayi bayan sun wuce Ceddi Plaza, dake Abuja.
Majiyar mu tace, masu binciken zasu tabbatar da ikirarin da Peter yayi na cewa yaji ihun neman taimako ne kafin yayi harbin da yayi sanadin rayuwar Igwetu.
DUBA WANNAN: Mare-mare a gidan gwamnati
Rahoton ya tabbatar mana za a binciki direban motan da kuma sauran mutanen dake cikin motar dalilin da ya hana shi tsayawa don gano dalilin take dokar yan sandan.
Yar uwar mai rasuwar, Chinenye tace yan sandan har yanzu basu fada musu dalilin harbin Igwetu ba da dan sandan yayi.
"Abinda kawai suka fada mana shine, suna bincike. Toh muna jiran su. "
Chinenye ta kara da cewa, akwai wasu mutane biyu a motar tare da yayarta, abin ya daure mata kai da sai dai yayan ta ta aka harba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng