Dukiyar da wasu manyan Sanatoci da Gwamnoni su ka samu ta sata za su koma hannun Gwamnatin Najeriya
Yaki da sata da Shugaba Muhammadu Buhari yake yi ya dauki wani sabon salo jiya bayan da aka kafa wasu dokokin yaki da satar dukiyar kasa. Yanzu Gwamnatin kasar za ta karbe dukiyoyin wasu manyan ‘Yan siyasa fiye da 100 da ake zargi ta sata aka same su.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa akalla tsofaffin Gwamnoni 11 da ake zargi sun mallaki wasu kadarorin su ta hanyar da ta sabawa doka za su yi asara. Wadannan Gwamnoni sun hada da Danjuma Goje na Gombe, da Adebayor Alao-Akala na Jihar Oyo.
Sauran Gwamnonin da Gamnati za ta karbe dukiyoyin su sun hada da Dr. Babangida Aliyu, Sule Lamido, Gbenga Daniel da kuma irin su Attahiru Bafarawa, Saminu Turaki, da Chimaroke Nnamani, da kuma Fintiri Amadu wanda yayi mulki a Adamawa.
KU KARANTA: Buhari ya sa hannu kan wata doka kan satar dukiyar kasa
Har wa yau kuma akwai wasu Ministocin kasar na baya wadanda ake zargi ta sata su ka samu dukiyoyin su da yanzu kayan su za su koma hannun Gwamnatin kasar. Daga cikin tsofaffin Ministocin akwai Adeseye Ogunleye da Jumuoke Akinjide.
Akwai kuma wasu da ake zargi sun saci kudin ne lokacin tsohon Shugaban kasa Jonathan irin su Bashir Yuguda, Abba Moro da Bala Mohammed. Sauran Ministocin da Shugaban kasar zai karbe kadarorin su su ne Femi Fani-Kayode da Nenadi Usman.
Jiya Shugaban PDP na kasa Prince Uche Secondus ya nemi Mutanen Ekiti su zabi Farfesa Olusola Kolapo Eleka na PDP inda yace idan su ka zabi APC ta Shugaba Buhari, Makiyaya za su yi ta kai masu farmaki su karbe masu kasa su hana su sakat.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng