Kamfanin Volkswagen za ta samawa dinbin Matasa aiki a Najeriya
Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa ana sa rai Kamfanin motocin Volkswagen za ta gina kamfaninta a Najeriya inda za a dauki sama da mutum miliyan 2 aiki a kasar.
Shugaban Kamfanin na Volkswagen Thomas Schaefer ya bayyana cewa da zarar Shugaban kasa Buhari ya sa hannu a wani kudirin da ya shafi harkar motoci a Kasar za a bude kamfanin kera motoci a cikin Najeriya.
Thomas Schaefer wanda shi ne Shugaban Kamfanin na Volkswagen yace a halin yanzu bai fi motoci 10, 000 ake kerawa a kasar ba. Da zarar an yi garambawul a dokokin da su ka shafi harkar motoci a kasar kasuwar za ta bunkasa.
KU KARANTA: An birne Marigayi tsohon Ministan Najeriya Ciroma
Kamfanin Volkswagen din ta na ganin cewa nan gaba za a iya kera motoci akalla 600, 000 zuwa 700, 000. Thomas Schaefer yace ana ma dai sa rai ana iya kera motoci 2, 000, 000 a duk shekara a Najeriya idan dokoki su ka canza.
Shugaban na Kamfanin Volkswagen yace shigo da motocin gwanjo da ake yi ke hana cigaba wajen kera sababbin motoci a kasar. Idan dai aka rika kera motoci a cikin gida, za a samawa dinbin Jama’a aikin yi inji Shugaban kamfanin.
Dazu kun ji cewa Shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari ya sa hannu kan wasu yarjejeniya na makudan miliyoyi na Dalolin kudi da Kasar Faransa kan wasu ayyuka da za ayi a Najeriya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng