Cikin Hotuna: An binne gawar Adamu Ciroma, tsohon minista daga 1979 zuwa 2011
A yau, Alhamis, 5 ga watan Yuli, ne Allah ya yiwa Malam Adamu Ciroma rasuwa a wani asibitin Turkish dake babban birnin tarayya Abuja.
An haifi Malam Adamu a ranar 20 ga watan Nuwamba, 1934 a garin Potiskum dake jihar Yobe, kuma ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.
Murtala Ramat Muhammed, tsohon shugaban kasa a mulkin soji ne ya nada Malam Adamu Ciroma a matsayin gwamnan babban bankin kasa (CBN) kafin daga bisani tsohon shugaban kasa a mulkin dimokradiiya, Alhaji Shehu Shagari, ya nada shi a mukamin minista daga 1979 zuwa 1983.
Tsohon shugaban kasa a mulkin soji, marigayi janar Sani Abacha, ya sake nada Malam Adamu Ciroma a matsayin minista kafin daga bisani Obasanjo ya kara nada shi a matsayin minista bayan dawowarsa mulki a matsayin shugaban kasa a mulkin dimokradiyya.
DUBA WANNAN: Da duminsa: Buhari ya yi doka a kan kadarorin gwamnati da aka kwato
Manyan mutane da suka hada da 'yan siyasa na jiya da na yau da wadanda suka rike mukamai a baya da masu rike da mukamai a yanzu ne suka halarci jana'izar Malam Adamu Ciroma da aka yi a Abuja.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng