Magen da tayi hasashen fitar da Najeriya daga kofin Duniya ta sheka lahira

Magen da tayi hasashen fitar da Najeriya daga kofin Duniya ta sheka lahira

- Magen nan da ta ce za’a fitar da Najeriya ta mutu muris har lahira

- Kasar Argentina dai ta samu nasara kan Najeriya da ci 2 – 1 a wasan cikin rukuni na gasar cin kofin Duniya da ake bugawa a kasar Russia 2018

- Sai dai bayan fitar da Najeriya suma kasar Faransa ta yi waje da su a gasar

Magen kasar China mai suna Baidian’er da tayi hasashen cire Najeriya daga gasar cin kofin duniya da yanzu haka ake bugawa a kasar rasha ta antaya zuwa barzahu.

Magen da tayi hasashen fitar da Najeriya daga kofin Duniya ta sheka lahira
Magen da tayi hasashen fitar da Najeriya daga kofin Duniya ta sheka lahira

Tun farko dai magen ta zabi kasar Argentina ne a matsayin wadda zata samu nasara a wasan cikin rukuni na D kafin buga wasan. Kuma zabin nata yayi daidai da yadda sakamakon gasar ya kaya na 2 – 1.

Kafin mutuwarta ta dai an rawaito cewa Baidian’er ta bayar da hasashen wasanni biyar wanda kuma duk su kayi daidai a gasar kofin duniyar, amma sai dai wasan Najeriyar shi ne na karshe da ta bayar a duniya.

KU KARANTA: Najeriya zata kai karar Lafari wajen FIFA

Magen mai suna Baidian’er kalar ruwan Lemo ce da rodi-rodin fari, kuma sunan nata da Hausa yana nufin rodi-rodin fari, sannan tana zaune ne a gidan ajiye kayayyakin tarihi na kasar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa saida da magen ta yi rashin lafiya kafin mutuwarta ta a ranar litinin. Kuma mutuwarta ta ya janyo tofa albarkacin bakin mutane kusan 10,000 a kafar sadarwa ta kasar.

Sai dai duk da zabarsu da wannan mage ta yi su ma kasar Argentina sun tattara komatsansu sun koma gida sakamakon cire su da kasar Faransa ta yi a gasar a zagaye na 16.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng