Mummuke: Yan Shia’a sun bullo da wata sabuwar salon yaki da jami’an tsaro

Mummuke: Yan Shia’a sun bullo da wata sabuwar salon yaki da jami’an tsaro

Hukumar tsaro ta sirri, DSS, ta fallasa wata kullaliyar tuggu da mabiya addinin Shi’a dake karkashin jagorancin shugabansu Ibrahim Zakzaky, inda suka shirya hanyoyin da zasu dinga bi wajen satar jami’an tsaro tare da yin garkuwa dasu, inji rahoton Daily Nigerian.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shirin da yan shi’ar ke yin a fara satar jami’an tsaro baya rasa nasaba da cigaba da garkame jagoransu da gwamnatin Najeriya ke yi, tun bayan kama shi da tayi a watan Disamba na shekarar 2015.

KU KARANTA: Ahmed Musa da Shehu Abdullahi sun baiwa marayu tallafin miliyan daya da buhu 100 na shinkafa

Takardar da hukumar DSS ta fitar tace: “Mabiya Shi’a sun kammala shirin fara yin satar jami’an tsaro tare da iyalansu, tare da yin garkuwa dasu sakamakon cigaba da tsare shugabansu El-Zakzaky, a yanzu sun fara gano gidajen jami’an tsaro, wuraren aikinsu da na iyalansu.”

Mummuke: Yan Shia’a sun bullo da wata sabuwar salon yaki da jami’an tsaro
Sanarwar

Idan za’a tuna ko a kwanakin baya sai da yan shia suka halaka wani jami’in Dansanda a yayin wani zanga zanga da suka yi a garin Kaduna, ranar da za’a cigaba da sauraron karar da gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da Zakzaky.

Sai dai da majiyarmu ta tuntubi Kaakakin Shia, Ibraheem Musa, ya musanta wannan zargi na hukumar DSS, inda yace, zargi ne kawai, kuma yace ba halinsu bane, basu taba tunanin yin hakan ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng