Yayan kirki: Ahmed Musa da Shehu Abdullahi sun baiwa marayu tallafin miliyan daya da buhu 100 na shinkafa

Yayan kirki: Ahmed Musa da Shehu Abdullahi sun baiwa marayu tallafin miliyan daya da buhu 100 na shinkafa

Fitaccen dan kwallon kafar Najeriya, Ahmed Musa tare da takwaransa Shehu Abdullahi sun tabbata yayan kirki, inda a ranar Laraba, 4 ga watan Yuli suka baiwa wasu marayu yan makaranta kyautar da ba zasu taba mantawa ba.

Jami’in kafafen sadarwar zamani na hukumar Zakkah da Wakafi na jihar Sakkwato, Mukhtar Haliru Tambuwal ne ya sanar da haka, inda yace yan kwallon biyu sun kai ziyara wata makaranta dake cike da yara marayu da suka rasa iyayensu a jihohin Yobe da Born a sakamakon rikicin Boko Haram, a garin Sakkwato, UK Jarma Academy.

KU KARANTA: Muhimman abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban APC Tawariyya

Yayan kirki: Ahmed Musa da Shehu Abdullahi sun baiwa marayu tallafin miliyan daya da buhu 100 na shinkafa
Tallafi

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yayin wannan ziyara, yan kwallon sun kai ma daliban kyautar kayan abinci da kudi, inda Ahmed Musa ya basu kyautar naira miliyan daya da rabi, yayin da Shehu ya basu kyautar shinkafa buhu dari, taliyar Indomi kwali hamsin, da kuma Lemun Kwlaba sinki ashirin.

Wannan aiki na alheri da Ahmed Musa da Shehu Abdullahi suka yi bai tsaya nan ba, inda Shehu ya baiwa yaran kyautar kayan kwallo (Jersey) kala biyu don amfaninsu wajen motsa jiki da wasanni.

Yayan kirki: Ahmed Musa da Shehu Abdullahi sun baiwa marayu tallafin miliyan daya da buhu 100 na shinkafa
Musa, Shehu da Maidoki

Daga cikin wadanda suka halarcin rabon wadannan kayayyaki, akwai mai gayya mai aiki, shugaban hukumar Zakkah da wakafi na jihar Sakkwato, Malam Muhama Lawal Maidoki wanda ya karbi wadannan kayayyaki, a madadin marayun, da shugaban makarantar, Jarman Sakkwato, Ummarun Kwabo.

Yayan kirki: Ahmed Musa da Shehu Abdullahi sun baiwa marayu tallafin miliyan daya da buhu 100 na shinkafa
Musa da marayun

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel