Muhimman abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban APC Tawariyya

Muhimman abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban APC Tawariyya

A ranar Laraba, 4 ga watan Yuli ne aka samu wani tsagin jam’iyyar APC karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano,Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ta bara’a da uwar jam’iyyar APC, inda ta kafa APC tawariyya, wanda ta lakaba ma suna ‘Gyararriyar APC’.

Ballewarta ke da wuya, sai APC Tawariyya ta nada tsohon dan gwagwarmaya, tsohon aminin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Buba Galadima a matsayin shugabanta, kamar yadda Legit.ng ta samu rahoto.

KU KARANTA: Zan cefanar da duk wani kadarar da muka kwato daga hannun barayin gwamnati – Buhari

Da wannan ne muka yi duba ga rayuwar Buba, musamman a siyasance don hako wasu muhimman abubuwa game da shi, da sabuwar turbar da ya dauka. Ga wasu daga cikinsu;

Muhimman abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban APC Tawariyya
Galadima

Aminin Buhari:Duk wanda ya san Buba, ya san shi tare da Buhari, haka zalika duk wanda ya san Buhari ya san shi tare da Buba Galadima, inda suka fara tarayyar siyasa tun a shekarar 2003, 2007, 2011 da 2015. Bugu da kari Buba Galadima ya yi kaurin suna a wancan lokaci wajen kare martabar Buhari.

Dan adawar Buhari: Sai dai wasu masana lamurran siyasa na ganin Buba Galadima da hannu cikin matsalolin da Buhari ya yi fama dasu a siyasa, wannan baya rasa nasaba da tsatstsamar dangantakar da ta bulla a tsakaninsa da Buhari, tun kafin zaben shekarar 2015. Don ko a zaben 2015 Kwankwaso ya yi.

Shima a nasa bangaren, Buba Galadima ya mayar da sukar Buhari a matsayin sabon aikinsa, inda yace har yanzu Buhari bai cika alkawari guda daya da yayi ma yan Najeriya ba, kuma yace Buhari ba zai iya mulkin Najeriya ba.

Jigon jam’iyyar APC da CPC: A gabanin zaben shekarar 2011, shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da hadin gwiwar Buba Galadima da sauran yan siyasa makusanta Buhari sun kafa jam’aiyyar CPC mai alkalami, wanda ya zama babban sakataren jam’iyyar na farko. Bayan zaben 2011, sai aka fara tattauna yadda za’a shiga zaben 2015, da wannan ne suka kafa jam’iyyar APC, shi ne sakataren jam’iyyar CPC na farko, haka zalika yana daga cikin jiga jigan yan siyasa mutum 9 da suka kafa APC.

Dan siyasar da ya fi shiga Kurkuku: Ta bangaren fuskantar tsangwama da cin zarafi kuwa, Buba Galadima bashi da na biyu a cewarsa, inda yace babu wani dan siyasa a Najeriya da ya sha wahalar da ya sha, saboda an kama shi, an daure shi kuma an kai masa hari sau Talatin da takwas.

Sai dai abin tambayar anan shi ne, ko APC tawariyya za tayi tasiri a zaben shugaban kasa na shekarar 2019?

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel