Buhari ya shirya kashe naira Tiriliyan 2.1 don kammala aikin wutar mambila
Ministan wutar lantarki, ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola, ya bayyana cewa a yayin da gwamnatocin baya ke ta surutu game da aikin tashar wutar lantarki dake Mambila jihar Taraba, shi kuwa shugaban kasa Muhammadu Buhari daukar aikin ya yi da muhimmanci, bayan shekaru 46 da farawa.
Fashola ya bayyana haka ne a yayin taron tunawa da tsohon dan gwagwarmaya, Herbert Macaulay, taron da ya kasance babban bako mai jawabi, a jami’ar Najeriya dake garin Nsukka, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.
KU KARANTA: Hikima: Yadda wani fasihin Yaro ya burge shugaban kasar Faransa da sana’arsa
“Ana iya cewa babu wata tashar wutar lantarki a duk fadin Afirka guda daya da ke bada wutar da tashar wutar Mambila za ta bayar idan an kammala aikinta, inda ake sa ran zata dinga fitar da 3,050mw, tare da kashe mata kudi naira biliyan 5.7, kimanin naira Tiriliyan 2.1 kenan.” Inji Fashola.
Dayake bayanin aikin, Fashola yace aikin na kunshe da madatsun ruwa daban daban, zai lakume miliyoyin tan na kankare, na rodi da siminita da sauran manya manyan kayan aiki.
“Wani muhimmin abu game da wannan aiki, shine tun a shekarar 1972 aka fara shi, sai dai babu abinda gwamnatocin baya suka yi game da shi banda surutu, har sai da Allah ya kawo Buhari ne aikin ya cigaba, wannan shine Canji!” Inji shi.
Sai dai Ministan ya bayyana matsalar kudi a matsayin babban kalubalen da suke fuskanta, sai dai yace batun neman kudin aikin na daga cikin batutuwan da shugaba Buhari ya tattauna da shugaban kasar China a yayin ziyarar da ya kai kasar a shekarar 2016.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng