Kwankwasiyya wahala – Inji wasu yan Kwankwasiyya da suka kona jar hula (Hotuna)

Kwankwasiyya wahala – Inji wasu yan Kwankwasiyya da suka kona jar hula (Hotuna)

A ranar Laraba, 5 ga watan Yuli ne wasu gugun matasan Kwankwasiyya suka shirya gangamin sanar da ficewarsu daga tafiyar jagoransu, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da babbaka jajayen hulunansu gaba daya, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

A yayin wannan gangami na wadannan tsofaffin yayan halaliyar tafiyar Kwankwasiyya sun sauya ma tsohuwar tafiyar tasu kirari, inda suka ce ta koma ‘Kwankwasiyya wahala’ daga ‘Kwankwasiyya Amana”

KU KARANTA: Jami’an hukumar Kwastam sun kama Motocin shinkafa guda 11 a jihar Kaduna

Kwankwasiyyah wahala – Inji wasu yan Kwankwasiyya da suka kona jar hula (Hotuna)
Kwankwasiyya

Wani ma’abocin kafarsadarwa zamani ta Facebook, Bashir Elbash ne ya daura hotunan matasan a yayin da suke banka ma hulunansu wuta, haka zalika ya daura hoton wani Dattijo da ya kekketa jar hularsa, wanda aka san duk wani dan kwankwasiyya na sawa

A wani labarin kuma, Sanata Kwankwaso tare da wasu magoya bayansa sun kafa APC tawariyyah, wanda suka kirata da suna ‘APC Gyara kayanka’, a karkashin jagorancin tsohon aminin shugaba Buhari, Buba Galadima.

Kwankwasiyyah wahala – Inji wasu yan Kwankwasiyya da suka kona jar hula (Hotuna)
Kwankwasiyya

Sai dai har zuwa yanzu ba’a tabbatar da inda siyasar shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, da ta Kaakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ta dosa ba, sakamakon nuna wariya da suka ce gwamnatin Buhari na musu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng