Ba mamaki Real Madrid za ta rabu da gwarzon ‘Dan kwallon ta

Ba mamaki Real Madrid za ta rabu da gwarzon ‘Dan kwallon ta

- Maganar komawa Ronaldo Kungiyar Juventus na kara karfi

- Juventus na ta kokarin sayen babban ‘Dan wasan na Duniya

Mun samu labari cewa akwai yiwuwar babban ‘Dan wasan Real Madrid Cristiano Ronaldo ya tashi ya koma Kungiyar Juventus Italiya don kuwa jita-jitar na kara karfi kawo yanzu.

Ba mamaki Real Madrid za ta rabu da gwarzon ‘Dan kwallon ta
‘Dan wasa Cristiano Ronaldo zai tashi ya bar Real Madrid

Sky Sports ta tabbatar da cewa Kungiyar Juventus na shirin lale kudi har fam Miliyan £88 domin raba Real Madrid da Gwarzon ‘Dan wasan gaban na ta mai shekaru 33. Kuma dai ba mamaki Real ta amince da wannan tayi na Juventus.

Real Madrid na iya saida babban ‘Dan wasan na ta na kasar Portugal idan har cinikin ya yiwu kamar yadda mu ke samun labari daga gidan Jaridun kasar Turai. Ana kishin-kishin din cewa ‘Dan wasan bai jin dadin zaman sa a Sifen.

KU KARANTA: Hukumar FIFA za ta dakatar da Najeriya daga wasa

Dama dai ‘Dan wasan na Duniya ya nuna cewa ba ya samun yadda yake so sai dai Real Madrid din ba tayi komai game da wannan maganar ba. Ana zargin cewa Shugaban Kungiyar watau Florentino Perez na ganin ya maida kudin sa.

A 2009 na Real Madrid ta saye ‘Dan wasan daga Manchester United kuma zuwan sa ya kawowa Kungiyar nasarori iri-iri. A Real Madrid din dai Ronaldo yayi nasarar cin kofi da kuma samun zama Gwarzon ‘Dan wasan Duniya ba sau daya ba.

Ba mamaki dai idan har Cristiano Ronaldo ya tashi, Real Madrid tayi kokarin sayen tsohon ‘Dan wasan Barcelona na Kasar Brazil Neymar Jr. ko kuma ‘Dan wasa Kylian Mbappe wadanda duk su ke bugawa gaban Kungiyar PSG na Kasar Faransa a yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: