Ya yi kokarin kashe kansa saboda rashin aikin yi, kotu ta tura shi gidan yari

Ya yi kokarin kashe kansa saboda rashin aikin yi, kotu ta tura shi gidan yari

Jami'an yan sanda na yankin Maroko dake Lekki a Legas sun kama wai Owolabi Ogunwande mai shekaru 27 a yayin da ya ke kokarin halaka kansa a Lekki Phase 1 ta hanyar rataye kansa.

Wanda ake zargin ya dauki matakin kashe kansa ne saboda ya gaza samun aikin yi tunda ya iso garin Legas a watan Mayun 2018 bayan ya baro jihar Osun.

Majiyar yan sandan ya ce wani jami'in Man 'O War mai suna Omotayo dake aiki a Lekki Concession Company ne ya ceto ran matashin ba dan haka ba da ya kashe kansa.

Kotu ta daure wani da ya yi yunkurin kashe kansa
Kotu ta daure wani da ya yi yunkurin kashe kansa

A yayin da yake bawa yan sanda labari, Ogunwade ya ce "Asali na dan garin Onyo ne daga jihar Osun kuma na zo Legas ne neman aikin hannu don in kula da kaina bayan na dena zuwa makaranta saboda iyaye na basu iya biya min kudin makaranra.

KU KARANTA: Yadda mai maganin gargajiya ya rasa ransa wajen gwajin maganin bindiga

"Na yanke shawarar kashe kaina ne a ranar 28 ga watan Yuni saboda nayi kokarin neman aiki tun watan Maris na shekarar 2018 amma hakan bai yiwu ba, na ma kasa samun kudin motar komawa gida."

An gurfanar dashi gaban kotun majistare dake Igbosere bisa laifuka biyu na yunkurin kashe kansa a Lekki toll gate da kuma sake yunkurin kashe kansa a caji ofis na yan sanda na Maroko ta hanyar amfani da igiya.

Dan sanda mai gabatar da kara, Cyriacus Osuji ya sanar da kotu cewa wanda ake tuhumar ya yi yunkurin kashe kansa a Lekki Toll gate da kuma Ofishin yan sanda na Maroko bisa dalilan da shi kadai ya sani.

Ya ce laifukan sun saba wa sashi na 235 na dokar masu manyan laifuka na jihar Legas na shekarar 2015.

Wanda ake zargi ya amsa laifinsa a kotu daga nan kuma alkalin kotu Majistare Aro Lambo ya dage cigaba da sauraron karar saboda a tabbatar da abin da ya faru da kuma yanke hukunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164