Dan sandan abokin kowa: Yadda wani dan sanda ya bayar da agajin gaggawa yayin wani hatsari (hoto)
Wani ma'abocin dandalin sada zumunta na Facebook mai suna Boye Abe ya yabawa wani dan sandan Najeriya da ya gano yana bayar da taimakon gagawa ga wani matashi da hatsari ya ritsa dashi cikin a dai-dai-ta sahu.
Matashin ya bayyana cewa wannan abin alkhairin da ya gani ya canja masa ra'ayinsa na da inda ya ke tunanin yan sandan kawai sun fi bayar da karfi ne wajen zartas da hukunci hakan yasa ya yi matukar mamaki.
Kamar yadda ya bayyana hatsarin ya afku ne a kusa da CMS Bus stop dake Legas a yau kuma ya yi amfani da wayarsa ta salula ya dauka hoton abin mamakin da ya gani.
KU KARANTA: Yadda mai maganin gargajiya ya rasa ransa wajen gwajin maganin bindiga
"Hatsarin ya faru ne tsakanin mai babur da a dai-dai-ta sahu (Keke Napep) kuma cikin kankanin lokaci sai wasu yan sanda dake sintiri kusa da wajen suka garzayo suka bayar da taimakon gagawa ga wanda hatsarin ya ritsa da su," Kamar yadda ya rubuta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng