Majalisar wakilai ta hana raba wa talakawa kudin Abacha

Majalisar wakilai ta hana raba wa talakawa kudin Abacha

Mambobin majalisar wakilai na tarayya sun bayyana rashin amincewarsu da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na raba wa talakawa $322 miliyan cikin kudaden Abacha da aka karbo daga kasashen waje.

Yan majalisan sun ce babu yadda za'ayi gwamnati tarayya ta kashe wadannan kudaden ba tare da amincewar majalisar ba.

A watan Yuni data gabata ne gwamnatin tarayyar ta bayyana cewa zata fara raba wa gidaje 302 a jihohi 19 wasu adadin kudade daga watan Yulin wanann shekarar.

Majalisar wakilai ta ki amince shugaba Buhari ya rabawa talakawa kudaden Abacha
Majalisar wakilai ta ki amince shugaba Buhari ya rabawa talakawa kudaden Abacha

A cewar gwamnatin tarayyar, wannan zai kasance cikin shirye-shiryen gwamnati na rage radadin talauci wanda ake sa ran zai fitar da miliyoyin 'yan Najeriya daga kancin talauci da fatara.

KU KARANTA: Abin al'ajabi: Ya ga matarsa da wani gardi a Legas shekara biyu bayan mutuwar ta

Sai dai 'yan majalisar suna tambayar gwamnatin tarayyar ta bayyana musu jimlar adadin kudin da aka karbo izuwa yanzu.

A zaman majalisar na ranar Laraba, 'yan majalisan sun nuna rashin gamsuwarsu kan wannan matakin da gwamnatin ta dauka, suna kuma juyayin yadda gwamnatin tarayyar zata iya tatance wane mutane ne ainihin talakawa dake bukatar taimakon.

Sai dai mai taimakawa shugaban kasa a fannin shari'a, Juliet Nwagwu tayi bayyani cewa gwamnati zata biya kudaden daki-daki ne saboda magance matsalolin tsafiye-tafiye.

Ta ce, "Babu wanda zai mika wa mutane tsabar kudi a hannu; za'ayi amfani da bankuna ne wajen biyansu kuma zamu tuntubi kungiyoyin sai kai masu rajjin cigaban al'umma don su sanya idanu a kan aikin,".

Sai dai su 'yan majalisar suna ganin cewa abinda ya dace shine a sanya kudaden cikin asusun harajin kasa sannan a raba shi ga dukkan jihohi a kan tsarin rabon arzikin kasa da aka saba amfani dashi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164