Haka kawai: Ban kaunar abin da zai jawo a rufe ni a kurkuku – Salomon Dalung

Haka kawai: Ban kaunar abin da zai jawo a rufe ni a kurkuku – Salomon Dalung

Ministan wasanni da matasa na Najeriya watau Barista Solomon Dalung ya bayyana cewa yana tsoron abin da zai kai shi shiga gidan yarin Kuje ana zaune kalau a Najeriya. Dalung ya bayyana wannan ne a wasikar da ya aikawa NFF.

Haka kawai: Ban kaunar abin da zai jawo a rufe ni a kurkuku – Salomon Dalung

Dalung ya nemi NFF tayi aiki da umarnin Kotu kar a jawo masa matsala

Ministan kasar ya bayyana wannan ne lokacin da ya aikawa Hukumar wasan kwallon kafa na Najeriya watau NFF wata takarda inda ya nemi Amaju Pinnick wanda shi ne Shugaban Hukumar ya sauka daga kan kujerar sa.

Gwamnatin Tarayya ta bakin Ministan shari'a ta umarci Amaju Pinnick da mukarraban sa su tattara su bar kujerar NFF inda aka nemi a maida Chris Giwa kan kujerar. Hakan dai zai sa a bi wani umarni da Kotu tayi kwanaki.

KU KARANTA: Ana daf da hana Najeriya buga kwallo a Duniya

Kun ji labaru cewa Minista Solomon Dalung ya nemi Hukumar NFF ta bi umarnin da babban Kotun Tarayya tayi a watan jiya inda Kotu ta nemi a dakata tukuna game da batun ingancin zaben su Pinnick da aka yi a 2014.

Alkali mai shari’a MH Kurya ne ya yanke wannan hukunci a babban Kotun Tarayya da ke Jos. Ministan kasar ya nemi NFF ta bi wannan doka na Kotu idan tana so a zauna lafiya inda yace shi ma bai son a daure sa a gidan yari.

A baya kun samu labari cewa akwai yiwuwar Hukumar kwallon kafa na Duniya watau FIFA ta dakatar da Najeriya daga buga kwallon kafa saboda wannan rikicin na Hukumar NFF. Ministan shari’a ne dai ya bada wannan umarni.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel