Nigerian news All categories All tags
Gagararren dan sara-suka kuma babban dillalin miyagun kwayoyi ya fada komar Yansanda a Sakkwato

Gagararren dan sara-suka kuma babban dillalin miyagun kwayoyi ya fada komar Yansanda a Sakkwato

Rundunar Yansanan jihar Sakkwato ta samu nasarar kama wani kasurgumin dan sara suka, kuma babban dillali tabar wiwi da sauran miyagun kwayoyi mai suna Aliyu Bello wanda aka fi sani da suna Aliyu KC, inji rahoton jaridar Punch.

Kaakakin rundunar Yansandan jihar, DSP Cordelia Nwawa ta bayyana haka a ranar Talata, 3 ga watan Yuni a yayin da take nuna ma yan jaridu mutumin da suka kama, inda tace tun shekaru hudu da suka gabata Yansanda ke farautar KC.

KU KARANTA: Yan Mata 4 sun gamu da ajalinsu a cikin wani madatsar ruwa na jihar Katsina

Aliyu KC

Aliyu KC

“Mun samu rahotanni da dama daga jama’a game da ayyuka yan sara suka a cikin garin Sakkwato, da wannan ne Yansanda suka shiga yaki da yan sara suka da yan daba, wanda hakan ya kaimu ga kama Aliyu KC tare da yarasa.” Inji ta.

Haka zalika tace akwai wani abokin gabar KC, mai suna Dahiru Abubakar Maibarewa da tace tuni suka kama shi, kuma a yanzu haka yana gidan Yari. A wani labarin kuma, Yansandan jihar sun kama wasu dillalan miyagun kwayo guda biyu, Musa Aiyu da Joseph David.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel