Auren soyayya ya mutu sakamakon musun kan wanda ya fi tsakanin Ronaldo da Messi

Auren soyayya ya mutu sakamakon musun kan wanda ya fi tsakanin Ronaldo da Messi

Wani mutumi dan kasar Rasha ya kashe aurensa da matarsa bayan wani zazzafan musu akan fitattun yan kwallon Duniya Messi, da Ronaldo, inda suke ja in ja da matartasa akan wa yafi iya kwallo, kamar yadda jaridar Argumentp Fakti ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito su dai wadannan ma’aurata mahaukatan masoya kwallon kafa ne, sai dai yayin da Mijin mai suna Arsen ke goyon bayan kungiyar Ajantina saboda Messi, ita kuwa matarsa, Lyudmila Portugal take goyon saboda Cristiano Ronaldo.

KU KARANTA: Babban dalilin da yasa n adage lallai sai na kai ziyara jihar Legas – Shugaban kasar Faransa

Ana cikin haka ne sai Mijin nata ya yi nuna farin cikinsa fiye da misali a ranar da Ajantina ta lallasa Najeriya a wasan karshe na rukunin D a gasar cin kofin Duniya, amma duk da haka Matsar ta tirje lallai Messi yafi Ronaldo.

Wannan lamari ya bakanta masa rai matuka, inda ya ga babu abinda yafi dacewa kamar ya rabu da matarsa tunda dai ta gagara bin abinda yake so, daga nan sai kawai ya tattara koamtsansa ya fice daga gidan, daga bisani kuma ya mika takardar neman kashe aurensa da Lyumdila ga Kotu.

Sai dai Arsen ya bayyana ma yan jarida cewa dama a yayin kallon gasar cin kofin Duniya na shekarar 2002 ne ya hadu da matarsa a wani gidan kallon kwallo, daga nan kuma soyayya ta kullu a tsakaninsu, wanda ta kai su ga aure.

“Tun da aka fara gasar cin kofin duniya take zagin Messi, wai ya kasa cin kwallo, ni kuma na kasa hakuri saboda irin kalaman da take fada akan Messi babu dadi, daga nan sai ni ma sai na zazzagi Ronaldo da duk wani kungiyar kwallon kafa da take so, kuma na kwashe kaya na bar gidan, na rabu da ita har abada.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng