Babban dalilin da yasa na dage lallai sai na kai ziyara jihar Legas – Shugaban kasar Faransa

Babban dalilin da yasa na dage lallai sai na kai ziyara jihar Legas – Shugaban kasar Faransa

Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya bayyana dalilinsa na dagewa akan lallai sai ya kai ziyara jihar Legas, shi ne don ya samu damar lekawa shelkwatar fitaccen mawakin Najeriya, Fela, wanda yace hakan na tuna masa rayuwa mai dadi da ya yi a baya.

Legit.ng ta ruwaito Macron ya yi zaman garin Legas, shekaru bakwai da mutuwar Fela, inda ya samu horo a ofishin jakadancin kasar a matsayinsa na babban ma’aikacin gwamnatin kasar Faransa. Yace a wancan lokaci shi ma’abocin zuwa gidan ne, gidan da yayi kaurin sun wajen shaye shayen wiwi da rawa tsirara.

KU KARANTA: Hattara dai! gwamnatin jihar Kaduna ta bullo da wata hanyar kawar da yan sara suka

A yayin amsa tambayoyi daga manema labaru a fadar shugaban kasa dake Abuja, Macron yace; “Da farko dai na dade ina neman damar dawowa Najeriya don sake kai ziyara gidan Fela, wuri ne mai alaka da tarihin nahiyar Afirka, kuma Fela da kaninsa Seun sun suna sosai a Faransa.

Babban dalilin da yasa n adage lallai sai na kai ziyara jihar Legas – Shugaban kasar Faransa
Shugaban kasar Faransa

Bugu da kari Macron ya bayyana aniyarsa na hada alakar inganta al’adun gargajiya tsakanin kasar Faransa da Najeriya, wanda yace hakan zai samar da ayyukanyi ga dimbin matasan Najeriya da basu da aiki.

Shima a nasa jawabin, shugaba Buhari ya bayyana gidan a matsayin wata akida mai kyau, wanda yace da ba don kyawunta ba, da tuni an manta da ita tun bayan mutuwar Fela Anikulapo Kuti.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel