Buhari bai taba cewa in ba wani mahaluki a Duniya rijiyar man fetur ba – Inji Kachiwku

Buhari bai taba cewa in ba wani mahaluki a Duniya rijiyar man fetur ba – Inji Kachiwku

Labari ya zo mana cewa karamin Ministan man fetur na kasa Dr. Ibe Emmanuel Kachikwu ya bayyana cewa tun da ya shiga ofis Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai taba kiran sa don a ba wani ta'aliki rijiyar man kasar ba.

Buhari bai taba cewa in ba wani mahaluki a Duniya rijiyar man fetur ba – Inji Kachiwku

Ibe Kachiwku yace Shugaba Buhari ya cika mai gaskiya

Karamin Ministan man fetur na Najeriya Emmanuel Kachikwu yayi wannan jawabi ne a wajen wani babban taro da aka shirya na masu ruwa da tsaki a harkar mai a Duniya. Ministan yace Shugaban kasar bai taba cewa a ba wane da wane rijiyar mai ba.

A cewar Dr. Ibe Emmanuel Kachikwu, rashin rabawa mutane rijiyar man kamar yadda aka saba a baya duk yana cikin kokarin da Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ke yi ne wajen yaki da cin hanci da satar dukiyar al’umma a Kasar.

KU KARANTA:

Ministan ya kara da cewa Shugaban kasar bai taba shiga cikin harkokin sa ba kamar ace ga wadanda za a ba kwangiloli a Ma’aikatar man fetur na kasar. Ibe Kachikwu yace hannun da Shugaban kasa ya sakan masa shiyasa ya iya aiki yadda ya dace.

A wajen taron dai Ministan ya bayyana irin kokarin da yayi lokacin yana rike da Kamfanin NNPC yake kuma cewa gas din Najeriya ya karu ya kuma bayyana cewa Najeriya tana da man fetur kusan ganga Biliyan 60 wanda zai ishi kasar na sama da shekaru 10.

Jiya kun ji cewa Jama’a sun fara huro wuta cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari wuta ya tsige manyan Sojojin kasar saboda kashe-kashen da ya ki ci ya ki cinyewa a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel