Na baiwa mahaifiyata Naira 50,000 a cikin kudin da muka yi fashinsu - inji wani dan fashi
- Bayan da asirin wani kasurgumin dan fashi ya tonu yayi wani jawabi mai ban mamaki
- Inda ya bayyana cewa mahaifiyarsa ma dai ta amfana da wannan sana'a ta shi
Wani shugaban yan fashi da makami mai suna Offor Joseph ya bayyanawa Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Lagos cewa ya baiwa Mahaifiyarsa kudi kimanin Naira 50,000 daga cikin Naira 900,000 da su ka yi fashinsa.
Joseph Offor wanda aka damke shi tare da wani mai suna Chinedu Ogu, ya bayyana yadda su ke samun bayanan sirri daga bankuna akan yadda mutane su ke fitar da kudi daga asusun su.
"Wannan ce satar da na yi a karo na 3, inda a karon farko mu ka yi fashin kudi da ya kai kimanin Naira 900,000 inda aka bani Naira 200,000 a matsayin ka so na, wanda ni kuma na yi amfani da kudin wajen magance matsalar yan uwana, inda na baiwa mahaifiyata naira 50,000 sai kuma kanwata naira 15,000, in ji Joseph".
Ya kuma kara da cewa akwai wani wanda ya ke musu sojan gona a cikin bankin, inda ya ke Lura da yadda hadadar kudi ke gudana a cikin bankin da ya ke yankinsu. Wanda shi wannan sojan gonar ne ya ba su bayanin yadda wani kwara ya cire wasu makudan kudi daga asusun ajiyarsa da ke bankin. Su kuma su ka bi shi, amma ba suyi nasarar yi masa fashin ba, bisa dalilin bace musu da ya yi.
KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun sace mutane 2 a Kaduna
Amma a karon karshe sun yi nasarar yi masa fashin a lokacin da ya ke kokarin shiga gidansa. Ya kuma bayyana yadda ya sayi bindigar da ya ke amfani da ita kirar libarba daga wani abokinsa dan jihar Bayelsa akan kudi kimanin Naira 35,000.
Tun da farko dai an damke wadannan yan fashin ne a ranar 25 ga watan Yunin da ya wuce, a lokacin da su ke dawowa daga wani fashi da su ka yi, inda su ka yi arangama da jami'an yan sanda.
A nasa bangaren Chinedu Ogu ya bayyana cewa, bai samu wani abin kirki ba a fashin da su ke yi, domin Naira 40,000 kawai ya samu. Kuma ya ce shi yana da aure amma kuma matarsa ba ta san yana fashi da makami ba.
An dai samu bindiga tare da harsasai masu rai guda 4 da kuma jaka da kudi a cikinta kimanin Naira 350,000, tare da takardar cire kudi a banki da kuma katin cirar kudi na ATM a gurin yan fashin.
Da ya ke magana kan wannan al'amarin kwamishinan yan sanda na jihar Lagos Imohimi Edgal, ya bayyana cewa yanzu haka suna tsaka da bincike, amma da zarar sun kammala binciken za su gurfanar da su a gaban kuliya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng