Yan Mata 4 sun gamu da ajalinsu a cikin wani madatsar ruwa na jihar Katsina
Rundunar Yansandan jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar wasu yan mata guda hudu a sanadiyyar wani hatsarin cikin ruwa da ya rutsa da su, inda kwalekwalen da suke ciki ya kifar dasu, kamar yadda kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar Lahadi, 1 ga watan Yuli karamar hukumar Kankara na jihar Katsina, yayin da yaran ke tafiya cikin wani kwale kwale a madatsar ruwa ta Mashigi.
KU KARANTA:
Kaakakin rundunar Yansandan jihar, SP Gambo Isah yace yaran na daga cikin mutanen kauyen Danzango da suka cikin kwale kwalen da nufin tsallakawa zuwa gefen ruwan, tare da yan kayayyakin da suka siya.
Haka zalika SP Gambo ya sanar da sunayen mamatan kamar haka;Yasira Suleiman, Shafawu Saidu, Firdausi Ibrahim da Rakiya Isa, dukkaninsu masu shekaru goma sha shida shida, sa’annan an garzaya da mutane biyu zuwa babban Asibitin Kankara, yayin da Maryam Zubairu da matukin kwale kwalen Abdullahi Muntari suka tsallake rijiya da baya.
Sai dai daga karshe, Kaakakin Yansandan yace babu laifin kowa a cikin wannan ibtila’I da ya faru, jarrabi ne daga Ubangiji Allah.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng