Abin al'ajabi: Ya ga matarsa da wani gardi a Legas shekara biyu bayan mutuwar ta

Abin al'ajabi: Ya ga matarsa da wani gardi a Legas shekara biyu bayan mutuwar ta

Wani mutum mai suna Okechukwu James Uwa ya yi ikirarin cewa ya hangi marigayiyar matarsa a kan babur tare da wani mutum a Legas.

Kamar yadda kafar intanet na Wuzup Nigeria ta wallafa, Uwa wanda dan asalin jihar Ebonyi ne ya ce yana hanyarsa ta zuwa Aba ne amma ya tsaya a Legas don ganawa da wani tsohon abokinsa kuma a nan ne ya ga matarsa a Oshodi.

Rainin hankali: Ya ga matarsa da wani gardi a Legas shekara biyu bayan mutuwar ta
Rainin hankali: Ya ga matarsa da wani gardi a Legas shekara biyu bayan mutuwar ta

A yayin da ya ke bayar da labari, Uwa ya ce, "Mata ne ta rasu sakamakon hastsarin mota shekatu biyu da suka shude kuma mun birne ta shiyasa nayi mamakin ganin ta tare da wani mutum a kan babur.

"Da farko na haufi sai daga baya nayi jarumta na kira sunanta amma tana juyo wa sai na neme ta na rasa."

Kamar yadda kafafen yadda labarai na intanet da dama suka ruwaito, mutumin dake dauke da ita a babur ya yanke jiki ya suma sai da aka farfado dashi.

Da aka masa tambaya game da matar, sai ya ce sun hadu ne a coci kuma sunyi watanni takwas suna tare.

Ya kuma ce sun tare a gida daya tun bayan haduwarsu a coci.

A cewarsa, "Ta fada min cewa ita ma'aikaciya ne a Legas kuma daga jihar Ebonyi ta ke. Sau da yawa na nemi in hadu da yan uwanta amma bata amince ba, tayi ta cewa yan uwanta basu da kirki."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164