A fusace wani mutumi ya kashe Babansa a sanadin kwartanci da Matarsa

A fusace wani mutumi ya kashe Babansa a sanadin kwartanci da Matarsa

Wani mutumi mazaunin kauyen Bazha dake lardin Matobo na kasar Zimbabwe, mai suna Steven Tshuma ya caccaka ma Babansa, kanin mahaifinsa wuka wanda ta yi sanadin mutuwarsa, bayan samun labarin kawun nasa na kwartanci da matarsa.

Jaridar The Nation ta ruwaito Tshuma ya fuskanci kawun nasa ne a wani dandalin shan giya game jita jitan dake yawo a gari na cewa wai kawun nasa mai suna, Pedzisai Mpofu na neman matarsa, Sinikiwe Moyo.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Yan bindiga sun bude ma jami’an Yansanda wuta a Abuja, sun kashe 7

Sai dai Kawun bai musanta ba, inda ya bayyana ma dan nasa cewwa gaskiya ne yana neman matarsa, kuma ma har yana alfahari da yin haka, kamar yadda majiyar Legit.ng ta samu rahoto.

Ai kuwa nan take Tshuma yace da wa Allah ya hada ni, ya durfafi kawun nasa, inda suka shiga dambe tare da baiwa hammata iska, wanda har ta kai ga Kawun ne neman samun galaba akan yaron nan, nan da nan shi kuma yaron ya zaro wuka daga aljihunsa, inda ya caka masa a wuya da baya.

Ba ko shuri Kawun ya fadi kasa matacce, don ko da aka yi kokarin garzayawa da shi Asibiti ya zubar da jini fiye da misali, don haka babu wani damar mika shi, sai dai aka isar da gawar tasa dakin ajiyan gawarwaki.

Amma fa shi ma Tshuma bai sha ba, don kuwa a yanzu haka Kotu ta kama shi da laifin kisa, inda ta yanke masa hukuncin zaman gidan Yari na tsawon shekaru ashirin da biyar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel