Hukumar FIFA na shirin dakatar da Najeriya daga wasan kwallo

Hukumar FIFA na shirin dakatar da Najeriya daga wasan kwallo

Mun samu labari cewa akwai yiwuwar Hukumar kwallon kafa na Duniya watau FIFA ta dakatar da Najeriya daga buga kwallon kafa saboda sabon rikicin da yake nema ya barke a Hukumar NFF mai kula da kwallon kafa na kasar.

A farkon makon nan ne Ministan wasanni da kuma kwadago watau Solomon Dalung ya umarci Shugaban Hukumar NFF na kasar Amaju Pinnick ya sauka daga mukamin sa. Dalung yace Ministan shari’a ne ya bada umarnin.

Solomon Dalung yayi wannan jawabi ne ta bakin wani mai magana da yawun sa. Ministan wasannin yace Abubakar Malami ya aiko masa takarda inda ya nemi Hukumar kwallon kasar ta NFF ta bi umarnin da Kotu tayi a baya.

KU KARANTA: EFCC tayi nasara kan wani 'Dan uwan Jonathan

Kotun Kolin kasar ta yanke hukunci cewa Amaju Pinnick ya sauka daga mukamin sa domin kuwa ba ta amince da zaben da ya kawo sa ba. Pinnick dai yayi kusan shekaru 4 a kan wannan kujera duk da rikicin da ake ta fama da shi a Kotu.

Hukumar FIFA ta Duniya dai ba ta son ganin Gwamnati ta shigo cikin harkar kwallon kafa. Da zarar an fara yi wa harkar kwallon haye, FIFA za ta iya dakatar da kasar gaba daya ta hana ta buga wasanni a Duniya kamar yadda aka nemi a yi a baya.

Dazu kun ji cewa har Najeriya ta fara shiryawa Gasar cin kofin Nahiyar Afrika da za a buga badi a kasar Kamaru. Idan FIFA ta dakatar da Najeriya dai Kasar ba za ta buga Gasar ba. Haka ma ‘Yan matan U-20 na kasar ba za su je Gasar Duniya ba na bana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Online view pixel