Kashe-kashen Filato: Anyi zanga-zangar neman kama T.Y Danjuma da Jona Jang a Hedikwatar 'Yan Sanda dake Abuja (hotuna)
- Wata kungiya ta bukaci a kama tsohon gwamnan jihar Filato Janah Jang saboda suna zarginsa da hannu cikin kashe-kashen Filato
- Kungiyar mai suna Middle Belt Peace Network da kuma nemi a bincike Janar Theophilus Danjuma
- A cewar kungiyar, Jang zai iya sanin sauran mutanen da ke da hannu wajen tayar da fitina a Jihar
Daruruwan mutane a karkashin kungiyar Middle Belt Peace Network sun gudanar da zanga-zanga a ranar Litinin 2 ga watan Yuli inda suke bukata a damke tsohon gwamnan jihar Filato Jonah Jang bisa zarginsa da hannu cikin kashe-kashen da akayi a kananan hukumomi uku a jihar.
Kungiyar ta bayar da wannan sanarwan ne yayin wata zanga-zanga da su kayi zuwa hedkwatan Yan sanda na Abuja a ranar Litinin, sun kuma bukaci a bincike dattijon Najeriya, Janar Theophilus Danjuma a kan afkuwar rikicin.
KU KARANTA: Matsalar tsaro: Gwamnoni na son a sauke su Buratai
Legit.ng ta gano gano cewa shugaban kungiyar, Jayeola Mohammed ta ce ya kamata shugaba Muhammadu Buhari ya cika alkawarin da ya dauka na kawo karshen kashe-kashen da hanyar umurtan jami'an tsaro su dauki matakan da suka dace.
Ga wani bangare daga cikin sanarwan nata: "Muna mika sakon ta'aziyar mu ga wadanda suka rasa yan uwansu sakamakon wannan fitinar kuma muna addu'a hakan ba zai sake faruwa ba.
"Muna kuma murna game da alkawarin da shugaba Buhari ya dauka na binciko wadanda ke da hannu a kashe-kashen don a hukunta su.
"Hakan yasa muke janyo hankalin shugaban kasa a kan zargin da ake yiwa tsohon gwamnan Filato, Sanata Jonah Jang da hannu cikin kashe-kashen da akayi a jihar cikin kwanakinan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng