Ruwa ya tafi da mutane 8 a jihar Niger
Hukumar 'yan sanda reshen jihar Niger sun bada sanarwar mutuwar mutane 8 sakamakon ruwa da ya cinye su a kauyen Rafin Gora a karamar hukumar Kontagora dake jihar
Hukumar 'yan sanda reshen jihar Niger sun bada sanarwar mutuwar mutane 8 sakamakon ruwa da ya cinye su a kauyen Rafin Gora a karamar hukumar Kontagora dake jihar.
Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Alhaji Dibal Yakadi, shine ya bayyanawa manema labarai a jiya, inda ya tabbatar da cewar an samo gawar mutane biyu a cikin su.
DUBA WANNAN: An kama wani dan sanda yayi kisa
Yakadi ya ce ruwan sama da aka yi mai karfi a ranar Litinin da yamma shine yayi sanadiyyar tafiya dasu.
Ya kara da cewa suna yi iya bakin kokarin su a yanzu haka domin ganin sun samo sauran mutum 6 da ba'a gani ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng