‘Yan gidan haya biyu sun yi fada kan bandaki, guda ya yiwa dayan wanka da ruwan zafi

‘Yan gidan haya biyu sun yi fada kan bandaki, guda ya yiwa dayan wanka da ruwan zafi

- Saurin fushi tsakanin mazauna gidan haya ya kaiwa guda ya baro

- Inda bayan kwararawa abokin fadansa an damke shi har an gurfanar da shi gaban alkali

- Amma sai dai ya ki amincewa da laifin da ake tuhumarsa da shi

Wata kotun majistire dake zamanta a Ikejan Jihar Lagos ta bayar da belin Sunday Freezer Wanda ake zargi da watasawa makocinsa ruwan zafi. An bayar da belinsa ne akan kudi kimanin Naira 100,000 tare kuma da wanda zai tsaya masa.

‘Yan gidan haya biyu sun yi fada kan bandaki, guda ya yiwa dayan wanka da ruwan zafi
‘Yan gidan haya biyu sun yi fada kan bandaki, guda ya yiwa dayan wanka da ruwan zafi

Tun da farko dai wanda ake zargi da aikata laifuffukan guda biyu suka hada da jikkatawa da kuma yunkurin lahantawa. Shi dai wanda ake zargin ma'aikacin wani kamfani dake a unguwar Oregun a yankin Ikeja.

Mai Shari'a a kotun majistiren Mista J. A Adegun ya bayar da shi beli ne bayan wanda ake zargin yaki amsa laifinsa.

KU KARANTA: Hukumar Hisbah ta cafke wasu 'yan mata 5 bisa laifin baɗala

A nasa bangaren dan sanda mai Gabatar da kara ya bayyanawa kotun cewa, wanda ake zargin ya aikata laifin ne ranar 24 ga watan Yunin da ya gabata a gidansu da ke unguwar Oregun. Ya kara da cewa an samu takaddama tsakanin Sunday Freezer da kuma makwabcinsa mai suna Reuben Afolabi akan amfani da bandakin da ya ke cikin gidan.

Inda daga nan ne Sunday ya watsawa Afolabi ruwan Zafi a kafadarsa hakan yasa ya samu rauni tare da lalata masa wayar tafi da gidanka wacce ta kai kimanin Naira 47,000,

Wanna dai laifi ne da ya saba wa sashe na 173 da kuma sashe na 350 na kundin dokar manyan laifuffuka ta jihar Lagos.

A karshe dai kotun ta Dage sauraron karar har sai ranar 10 ga watan Yulin nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng