Babban kalubalen da dan sanda ke fuskanta a Najeriya – Tsohon IG Suleiman Abba
- Tsohonn shugaban rundunar ‘yan sanda ta kasa, Suleiman Abba, ya yi Magana a kan kalubalen dad an sandan Najeriya ke fuskata
- Abba ya bayyana cewar daya daga cikin kalubale da jami’an ‘yan sanda ke fuskanta shine jama’ar Najeriya basu yarda da su ba
- Ya bayyana cewar akwai bukatar jami’an ‘yan sanda suke aiki tare da jama’a domin samun nasara a kokarinsu na kawo zaman lafiya
Tsohon shugaban rundunar ‘yan sanda ta kasa, Suleiman Abba, ya bayyana cewar babbar matsalar da jam’ian ‘yan sanda ke fuskanta shine, jama’a basu yarda da su ba.
Da yake ganawa da manema labarai a jiya, Lahadi, 1 ga watan Yuni, Abba ya bayyana cewar akwai bukatar a inganta albashin jami’an ‘yan sanda duk day a bayyana cewar, karancin albashi ko rashin biyan albashi a kan lokaci, bai kamata ya zama uzuri ga jami’an domin aikata ba daidai ba.
DUBA WANNAN: Rikicin jihar Filato: Muna sane sarai da abinda ake son kullawa - CAN
Abba ya bayyana cewar, matsalar albashi ba it ace babbar matsalar dan sandan Najeriya ba. Sannan ya kara da cewa, “kulawa da hakkin dan sanda bayan ya bar aiki, musamman kulawa da karatun yaransu da muhallin da zasu zauna, shine babban kalubale.”
Tsohon IG Abba ya yi aiki a sassan hukumar ‘yan sanda daban-daban kafin daga bisani a nada shi ya jagoranci rundunar ‘yan sanda ta kasa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng