Rikicin Filato: Bayan kashe mutane 10 tare Sojoji sun damke wasu mahara a jihar Filato
- A kalla Sama da mutane goma ne su ka rasa rayukansu cikin karshen makon da ya gabata a jihar Filato
- Jihar Filato dai na fama da tashin hankali tun bayan da wasu 'yan bindiga suka sarki kai hare-hare a wasu sassan jihar
- Harin baya-bayan nan da aka kai dai Sojoji sun samu galabar kama mutane 4 daga cikin maharan
Harin da aka kai karamar hukumar Mangu da Barkin Ladi ya sanya rundunar tsaron sojoji ta musamman komawa da matsuguninta yankin Barkin Ladi da zama domin dakile sake afkuwar hakan a nan gaba.
Da farko dai kimanin mutane 6 me su ka mutu a wani hari da ‘yan bindigar suka kai ranar asabar a yankin karamar hukumar Mangu. Sai kuma wasu 4 da aka kashe washegarin ranar su kuma daga yankin karamar hukumar barkin Ladi.
KU KARANTA: Rikicin Plateau: Mutane sun fara kaura daga gidajensu
Wadannan hare-hare na zuwa ne bayan mummunan harin ranar 23 ga watan Yunin da ya gabata. Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin Mnajo Adam Umar wanda shi ne shugaban rundunar Sojoji ta musamman don wanzar da zaman Lafiya.
Ya bayyana cewa duk da dokar hana fita da aka sanya a yankin, da kuma irin kokarin da jami'an Sojoji ke yi, amma hakan bai hana wasu bata gari kai wannan harin na ta'adanci a yankin marabar Kantoma da ke karamar hukumar Barkin Ladi ba.
Da misalin karfe 3 na daren ranar lahadi ne jami'an Sojojin da ke Dorawa su ka samu kiran neman agajin gaggawa daga yankin. Inda aka sanar da su halin da ake ciki, daga nan sojojin su ka garzaya wannan yankin inda bayan artabu da ‘yan bindigar su ka yi nasarar damke 4 daga cikin maharani wasu kuma suka tsere da raunuka.
Manjon ya kuma sha alwashin kawo karshen abin da ke faruwa na kashe-kashen mutane da ake yi ta hanyar ribanya kokarin jami'ansa. Sannan ya kuma bukaci al'ummar yankin da su cigaba da bayar da hadin kai da kuma sanar da duk wani abu da ba su aminta da shi ba.
A karshe ya gargadi masu kai hare-haren da kakkausar murya domin babu shakka zai fada komarsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng