Hannun wani matashi da ‘yan sanda suka yiwa dukan tsiya ya fara rubewa, kalli hotuna
Wani matashi, Saminu Ibrahim Magoli, dake zaune a unguwar Usubu ta karamar hukumar Kontagora a Jihar Neja na neman rasa hannunsa na hagu sakamakon dukan da jami'an 'yan sanda na ofishin shiyyar B a Kontagora suka yi masa.
Saminu, wanda ke sana'ar wankin mota, shine ke rike da ragamar gidansu kasancewar iyayensa marasa karfi ne, kamar yadda Rariya suka rawaito.
Da yake shaidawa Rariya yadda lamarin ya faru, Saminu ya ce, "Ina wurin sana'a ta, wankin mota, ranar Sallah sai ga wasu mutane sun zo suna tambayar wani abokin aikina, Muhammad Tauhid M.T, sai nace masu bani da masaniyar inda yake domin yakai kimanin kwanaki 5 bai fito wurin aiki ba, daga fadin haka sai kawai suka kama ni suna kokarin jefani a motar su, na ce masu ni b azan je ko ina ba tunda banyi laifin komai ba wanda kuma suke nema bansan laifin da yayi ba.
"Muna cikin hakan saiga wanda suke neman sai nace masu ga shi nan ya zo, shi kuma yana ganinsu saiya sheka da gudu, suka bishi basu yi nasarar kamashi ba, sai suka jefani mota ta karfin tsiya suka wuce da ni ofishin su,” Inji Saminu
Sannan ya cigaba da cewar "Da zuwanmu suka saka ni a Sel suka kulle, can saiga wani dan sanda ya zo da gora ya hau duka na har ya karya mani kafada, duka na kawai yake yi ko ta ina gashi ina fama da ciwon yatsa (Karkare). Duk jikina sida ya kumbura amma duk da hakan nan suka barni har gari ya waye.
DUBA WANNA: Mutane 5 sun mutu a wani rikici da ya barke tsakanin fusatattun mahauta da ‘yan sanda
"Da 'yan uwana suka zo sai sukace sai an bayar da kudin beli sannan zasu sake ni, da dikyar suka karbii dubu goma(N10,00).
“Bayan mundawo gida aka kira mai dori ya min dori a hannu, yau sama da kwana 15 bana iya bacci, ga hannuna ya kumbura yana kokarin rubewa gashi kuma iyayena talakawane ko abunda zamuci saina fita na nemo,” Sami ya fada cikin damuwa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng