Binciken musamman ya nuna cewa ana ganin fa’idar N-Power
Mun samu labari cewa wani bincike da Jaridar Premium Times tayi ya nuna cewa tsarin nan da Gwamnatin Shugaba Buhari ta kawo na tsarin N-Power yana taimakawa al’umma ta hanyoyi da-dama.
Gwamnatin Buhari tayi kokarin inganta rayuwar al’umma wanda daga cikin yadda aka shirya cin ma wannan buri akwai tsarin N-Power. Bayan nan kuma dai ana rabawa wasu da talauci yayi wa katutu kudi domin su rage zafi.
Tsarin na N-Power da aka kirkiro a 2016 ya ci Naira Biliyan 26. An dauki Matasa da su ka kammala karatun gaba da Sakandare har 200, 000 aiki ne ta wannan tsari inda aka aika wasu zuwa Makarantun Boko domin su koyar.
KU KARANTA: An yi ram da wani gagararren 'Dan fashi a Najeriya
A wasu Makarantun dai dama ana fama da karancin Ma’aikata, sai dai binciken da Jaridar Premium Times tayi ya nuna cewa an sharewa wasu da dama daga cikin irin wadannan Makarantu kukan su ta sanadiyyar aikin nan na N-Power.
Matasa da dama da aka dauka aikin yanzu su na koyar da yara a Makarantun Firamare da ma Sakandare. Wasu kuma dai sun zama Malaman gona ne yayin da aka zabi wasu domin aikin kiwon lafiya da kuma kaninkanci da sauran su.
Kungiyar NUT ta Malamai ta koka da tsarin na N-Power lokacin da Gwamnatin Buhari ta bullo da shi. Sai dai a wasu Makarantun da ke Garin Ado-Ekiti a Jihar Ekiti, da aka yi bincike an gano cewa N-Power din yana taimakawa ‘Dalibai matukar gaske.
Kun san cewa bayan nan kuma Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta kawo wani tsari na ciyar da abinci ga Kananan Yara da ke Makarantun Firamare a wasu Jihohin Kasar. Hakan ya taimaka wajen samun karuwar masu shiga Boko.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng