Takaitaccen tarihin Gwarzon ‘Dan wasan Najeriya Ahmed Musa
2 - tsawon mintuna
Gwarzon ‘Dan wasan nan na Kungiyar Super Eagles na Najeriya watau Ahmed Musa yayi suna a Duniya don haka mu ka kawo maku kadan daga cikin tarihin babban ‘Dan kwallon.
- An haifi Ahmed Musa ne a Watan Oktoba a shekarar 1992 a Garin Jos da ke Jihar Filato. Tun yana ‘Dan shekara 14 dai Ahmed Musa ya fara nunawa Duniya irin kwarewar sa a Kulob din GBS da ke Jos.
- A shekarar 2007 ne aka fara sanin ‘Dan wasa Ahmed Musa a Duniya wanda hakan ta sa Kungiya kwallon kafa na JUTH da ke Jos ta dauke sa. A nan kuma Ahmed Musa ya kwallaye har 4 a shekarar.
- Bayan JUTH ne Ahmed Musa ya koma Kungiyar Kano Pillars a matsayin ‘Dan wasan aro. A Kano Pillars ne dai Musa ya kafa tarihi ya ci kwallayen da ba a taba cin su ba a Gasar Firimiya na Najeriya.
KU KARANTA: Jakadan Ingila yayi magana game da Najeriya
- A 2010 ne Musa ya koma Kungiyar Turai ta VVV Venlo sai dai bai iya fara bugawa ba sai da ya cika shekara 18 a Duniya. A wasan da ya fara bugawa kuwa ya nuna kan sa inda ya samowa Kungiyar sa finariti.
- Bayan nan ne dai Tauraruwar Musa ta rika haskawa har ta kai Kungiyar CSKA Moscow su ka saye sa a 2012 bayan wasu da dama sun yi kokarin sayo ‘Dan wasan. Bayan shekaru kadan ne kuma ya koma Leicester City na Ingila.
- A gida kuma dai Ahmed Musa ya nuna kwarewar a Super Eagles inda ya ci kwallo 2 a wasan Najeriya da Kasar Argentina a 2014. A Gasar cin kofin na Duniya da ake yi a bana ma dai Musa ya sake zura kwallaye 2.
- Ahmed Musa dai ya auri Jamila wanda ta haifa masa ‘Ya ‘ya 2. Daga baya dai su ka rabu bayan sun samu sabani a Ingila. Musa ya koma ya auri Juliet Ejue wanda ta fito daga Kudancin Najeriya
- Babban 'Dan wasan kwallon gaban na Kungiyar Leicester City Ahmed Musa dai mutum ne mai taimakon jama’a a Kano da ma Najeriya baki daya.
- Ahmed Musa Musulmi ne wanda ya kuma rike addinin sa domin kuwa a kan gan shi a Masallaci da sauran wuraren ibada cikin kayan addini.
- Babban 'Dan wasan ya taba rike Kyaftin din Super Eagles kuma shi yake goya lamba 7. Kafin nan Musa ya buga Kungiyar U-21 na Najeriya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng
Tags: