Abin tausayi: Mutane 10 sun mutu a hadarin hanyar Kano da ya faru a yau

Abin tausayi: Mutane 10 sun mutu a hadarin hanyar Kano da ya faru a yau

A kalla mutane goma ne suka rasu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru babban titin Kaduna zuwa Kano a yau Asabar.

Kamfanin dillanci labarai na kasa (NAN) ta ruwaito cewa hatsarin ya faru ne misalin karfe 5.30 na asuba kusa da Nuhu Bamalli Polytechnic dake Zaria.

Shugaban sashin wayar da al'umma na hukumar kiyaye haddura na kasa (FRSC) na Zaria, Idris Yahaya ya tabbatar da afkuwar lamarin mai ban tausayi.

Abin tausayi: An mutu a hadarin hanyar Kano zuwa Kaduna
Abin tausayi: An mutu a hadarin hanyar Kano zuwa Kaduna

KU KARANTA: Yadda wata matan aure ta kashe mijinta saboda ya ce zai yi mata kishiya

Hatsarin da ya ritsa da motocci uku, babban bus mai lamba GDD 361 YE da karamar mota mai lamba SGR 57 XA da kuma wata motar alfarama mai lamba LND 246 XE.

Mutane 48 ne ke cikin motocci ukun, mutane tara sun kone kurmus, yayin da wata mata daya ta mutu a asibiti. Sauran 31 sun sami raunuka kuma suna karbar maguguna sai mutane bakwai kuma sun tsira.

Direban babban bus din yana karbar magunguna a asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello da ke Shika a Zaria.

Kwamandan hukumar FRSC din ya ce dukkan wanda suka sami rauni suna asibiti, yayin da gawawakin wadanda suka rasu yana dakin ajiye gawa na asibitin.

Mr Zubairu ya shawarci direbobin da suke tafiya mai nisa su rika tsayawa suna mike kafafuwarsu bayan sunyi tafiyar sa'o'i hudu saboda gajiya.

Ya kuma shawarci direbobin su kula da yadda suke tuki musamman wannan lokacin daminan tare da tabbatar da cewa tayoyin motoccin su na da kyau musamman masu tafiya mai tsawo domin yin doguwar tafiya da tsaffin taya na da hatsari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164