Matsalar tsaro: Gwamnoni na son a sauke su Buratai

Matsalar tsaro: Gwamnoni na son a sauke su Buratai

Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun ce zasu bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya sauke dukkan shugabanin hukumomin tsaro muddin suka kasa kawo karshen kashe-kashen da akeyi a kasar.

Sai dai gwamnonin sun ce suna son su zauna tare da shugabanin hukumomin tsaron don su bayyana musu yadda kashe-kashen ke haddasa kiyaya tsakanin al'umma.

A yayin da ya yi jawabi jiya a Jos, ciyaman din kungiyar gwamnonin Najeriya, Abdulaziz Yari na jihar Zamfara ya ce dole shugabanin hukumomin tsaron su zage damtse idan ko ba haka ba "zamu bukaci shugaban kasa ya sawake musu".

Matsalar tsaro: Gwamnoni na son a sauke su Buratai
Matsalar tsaro: Gwamnoni na son a sauke su Buratai

KU KARANTA: Tambuwal ya yi magana a kan alakanta shi da kashe-kashen jihar Filato

Yari ya yi wannnan jawabin yayin da ya jagoranci tawagar gwamnonin karkashin kungiyarsu (NGF) a ziyarar jaje da suka kai wa gwamna Simon Lalong na Filato sakamakon kashe mutane 86 da makiyaya su kayi a wasu sassan jihar.

Anyi kashe-kashen ne a garin Barkin-Ladi da Riyom da ke karamar hukumar Jos ta Kudi a ranar Lahadi 24 ga watan Yunin shekarar 2018.

Gwamnonin sun jadada cewa ya zama dole a hada karfi da karfe wajen ganin an magance kashe-kashe domin ba za su saka idanu suna kallo ana yiwa al'ummarsu irin wannan zaluncin ba.

"Muna kira ga shugaban kasa ya hukunta dukkan wanda aka samu da hannu cikin kashe-kashen.

"A matsayin mu na shugabani, dole mu dauki mataki yanzu idan ba haka ba masu kashe-kashen za su iso kan mu," inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164