World Cup: Saboda in yi ido biyu da Lionel Messi na yi tattaki zuwa Rasha – Clifin Francis

World Cup: Saboda in yi ido biyu da Lionel Messi na yi tattaki zuwa Rasha – Clifin Francis

Wani Bawan Allah mai suna Clifin Francis ya bayyana yadda ya tako tun daga Kudancin Kasar Indiya zuwa kallon Gasar cin kofin kwallon kafa na Duniya da ake bugawa a Kasar Rasha.

World Cup: Saboda in yi ido biyu da Lionel Messi na yi tattaki zuwa Rasha – Clifin Francis
Wani mutumin Indiya ya tafi Rasha a keke saboda World Cup

Clifin Francis Malamin lissafi ne a wata Makaranta a Kasar Indiya kamar yadda BBC ta bayyana. Sai dai bai da kudin da za su isa ya tafi zuwa Rasha kallon wasanni. Shi dai wannan mutumi yace don haka ya nemi keke domin ya rage kashe kudi.

KU KARANTA: An kama dillolin kwaya da-dama a Najeriya

Abin da ya ba mutane mamaki shi ne yadda Clifin Francis ya shirya tafiye-tafiyen sa a farkon shekarar nan. Francis ya tafi Dubai ne a jirgi wanda daga nan ya wuce Kasar Iran a kwale-kwale. Daga nan kuma ya kama tafiya a kan keke zuwa Rasha.

Wannan mutumi ya sha wahala kwarai a hanya a tafiyar da yayi mai kilomita 4200 inda har ta kai sai da ya rame ya kuma saye wani sabon keke. A wasu kasashen ma dai da kyar ya shiga inda aka tsaya yi wa takardun tafiyar su kallon kwakkwafi.

Kusan a kowace rana ta Allah Francis ya kan samu sama da Naira 14, 000 a inda yake aiki don haka ya shirya domin haduwa da gwarzon sa Lionel Messi. A wasan Kasar Iceland ma dai Messi ya barar da finariti wanda masoyin na sa bai ji dadi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng