Mutane 5 sun mutu a wani rikici da ya barke tsakanin fusatattun mahauta da ‘yan sanda
Wata zanga-zanga da kungiyar mahauta suka gudanar jiya a Ibadan saboda canjawa kasuwar su matsuguni ta rikide zuwa rikici day a yi sanadiyar mutuwar mutane biyar.
Kazalika, masu zanga-zangar sun kone wani ofishin hukumar ‘yan sanda dake cikin kasuwar tare da wasu motoci biyar dake ajiye a harabar ofishin. Barkewar wannan rikici ne ya saka gwamnatin jihar bayar da umarnin rufe kasuwar cikin gaggawa.
An samu barkewar rikici ne bayan fusatattun mahautan dake zanga-zanga sun far wa jami’an ‘yan sandan da aka turo domin rufe kasuwar kwata ta Bodija. Lamarin day a haifar da hargitsi a tsakani tare da nakasa harkokin cinikayya.
Tunda farko, gwamnatin jihar ta Oyo ta umarci mahautan da su koma sabuwar kwatar zamani da ta gina a kauyen Amosun dake karamar hukumar Akinyele. Gwamnatin jihar ta bayyana cewar, bata yarda da duk wata kwata dake jihar ba bayan sabuwar da ta gina.
DUBA WANNAN: Tuna baya: Takaitaccen tarihin sadauki, Hassan Sarkin Dogarai
Gardamar wasu daga cikin mahautan na kin komawa sabuwar kasuwar ya saka ta garzaya kotu tare da samo izinin rufe kasuwar.
Shugaban kungiyar mahauta na yankin kudu maso yammacin Najeriya, Mista Biliaminu Eleshinmeta ya bukaci gwamnatin jihar da ta gudanar da bincike domin gano masu hannu cikin rikicin day a barke tare da bayyana cewar, wasu batagari ne suka fake da zanga-zangar mahautan domin tayar da tarzoma.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng