Tsohon mataimakin shugaban kasar Ghana ya mutu yayin atisayen sanyin safiya

Tsohon mataimakin shugaban kasar Ghana ya mutu yayin atisayen sanyin safiya

Tsohon mataimakin shugaban Ghana, Kwesi Amissah-Arthur ya fadi ya mutu a lokacin da ya ke atisayensa na safe kamar yadda jaridun kasar suka ruwaito.

An ruwaito cewa Amissah-Arthur wanda ya yi aiki tare da tsohon shugaban kasa John Mahama ya yanke jiki ya fafi ne a gidan motsa jiki na sojin saman kasar.

An garzaya dashi asibitin sojoji na 37 inda a can ne ya rasu bayan kankanin lokaci.

KU KARANTA: Kuma dai: An sake hatsarin mota a Legas, an rasa rayyuka biyu

Tsohon mataimakin shgaban kasar wanda akafi sani da PK ya kuma yi aiki a matsayin gwamnan Bankin Ghana daga shekarar 2009 zuwa 2012 kuma a wannan lokaci ne tattalin arzkin Ghana ya kasance yana bunkasa na tsawon watanni 30.

Ganin da al'umma suka masa na karshe shine a ranar Laraba a wajen wani taron kaddamar da littafin da matarsa Matilda Amissah-Arthur ta wallafa.

Shugaban kasar Ghana, Addo Akufo-Addo ya yi ta'aziyar rasuwar Amissah-Arthur a shafinsa na Facebook inda ya bayyana marigayin a matsayin ma'aikacin gwamnati wanda ya dade yana gudanar da aikinsa cikin mutunci da karamci.

Ya kuma ce rasuwar tsohon mataimakin shugaban kasar abu ne da ya sosa masa rai sosai.

Amissha-Arthur ya kasance malami ne mai koyar da tattalin arziki a kwallejin ilimi na jihar Anambra da kuma jami'ar Ghana da ke Legon.

Daga bisani kuma ya yi aiki a matsayin mataimaki na musamman ga tsohon ministan kudi, Kwesi Botchway daga shekarar 1983 zuwa 1986.

Marigayin ya rasu ya bar matar aure daya Matilda da yara biyu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164