Kotu ta wanke tsohon Gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido
- Kotu ta nemi ayi watsi da zargin da ke kan Sule Lamido
- Jihar Jigawa ta maka Tsohon Gwamnan na PDP a Kotu
- Ana zargin Tsohon Gwamnan da tada fitina da hayaniya
Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa wata Kotu da ke Garin Dutse a Jihar Jigawa ta wanke tsohon Gwamnan Jihar da ake ta faman shari’a da shi tun a 2017.
Gwamnatin Jihar Jigawa ce ta maka tsohon Gwamnan a wata Kotun Majistare kwanaki inda ta ke zargin sa da laifin tada rikici da hayaniya da kuma batawa wasu suna. Lauya Yakubu Ruba ne dai wanda ya kare Alhaji Sule Lamido a Kotu.
KU KARANTA: Kotu ta sake yin dumu-dumu da tsohuwar Ministar PDP
Usman Mohammed Lawal wanda shi ne Alkali mai shari’a a karamin Kotun ya yanke hukuncin a cigaba da shari’ar. Bayan nan ne Lauyan da ke kare tsohon Gwamnan ya tafi babban Kotun Jihar inda ya nemi a daga karar zuwa nan gaba.
Alkali mai shari’a Ahmed Musa Gumel da sauran Abokan aikin sa Umar Sadiq da Abdulhadi Suleiman a babban Kotun Jihar sun yanke hukuncin cewa ayi watsi da shari’ar inda ta nemi Kotu ta watsar da duk tarin zargin da ke kan sa.
Dazu mu ka ji cewa Jam’iyyar adawa ta Jam’iyyar PDP ta zargi APC da kashe makudan kudi har kusan Naira Biliyan 4 wajen babban taron Jam’iyyar mai mulki da aka yi kwanan nan a Birnin Tarayya Abuja.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng